By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaro da ma’aikatan ceto na can na neman gawarwakin mutane a wurin da wani bam ya tashi a birnin Mogadishu na kasar Somalia a yau Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021.
Shaidun gani da ido sun ce wata babbar fashewa ta afku a wani yanki mai cike da cunkoson jama’a na babban birnin kasar Somaliya da sanyi safiyar yau.
Akalla mutane 5 ne aka tabbatar sun mutu yayin da wasu fiye da 10 suka jikkata sakamakon wani harin bam da aka kai da mota kusa da wata makaranta a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a ranar Alhamis, in ji wani jami’in tsaro.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa harin dai shine na baya-bayan nan da aka kai a kasar mai fama da rikici.
“An samu fashewar bam a cikin wata mota an tabbatar da mutuwar mutane biyar sannan wasu goma sha biyar suka samu raunuka,” kamar yadda jami’in tsaro Mohamed Abdillahi ya shaidawa AFP, ya kara da cewa dalibai na cikin wadanda suka jikkata.