Mutane 16 ne suka kone kurmus a ranar Talata a lokacin da wata karamar motar bas da wata mota kirar SUV suka yi karo a kan wata babbar hanya a lardin Limpopo da ke arewa maso gabashin Afirka ta Kudu, in ji wani jami’in yankin.
Mai magana da yawun ma’aikatar sufurin lardin Mike Maringa ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa direban SUV ya rasa iko sarrafa motar ne bayan da tayar motar ta fashe kuma ta yi karo da wata motar bas mai mutane 22 mai suna Mercedes-Benz.
“Bas din ya wuta kuma mutane 16 da suka makale a ciki sun kone da ransu,” in ji shi.
Direban SUV ya mutu a yayin afkuwar lamarin, in ji shi. Wasu mutane takwas sun tsira da raunuka.
Kananan motocin haya masu zaman kansu jama’a masu zirga-zirga a Afirka ta Kudu ke amfani da su sosai.
Duk da kasancewar daya daga cikin manyan hanyoyin sadarwa na zamani a nahiyar Afirka ta Kudu na da daya daga cikin mafi muni a duniya game da amincin hanyoyin, lamarin da galibi ake zargi da tukin mota mara kyau na ganganci.
Kusan mutane 1,500 suka mutu akan tituna a lokacin bukukuwan Kirsimeti, a cewar gwamnati.