Aniekan Inuk Effiong, wani jami’in ne mai kula da zirga-zirgar jiragen sama a filin sauka da tashin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas ya rasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa Effiong ya rasu ne a bakin aiki a safiyar ranar Litinin.
An gano cewa Konturola din yana da shekaru 40 a duniya ya fadi a lokacin da yake bakin aiki a cikin filin jirgin saman Legas.
Duk da dai kawo yanzu ba a samu tabbacin mutuwarsa a hukumance ba, wata majiya a filin jirgin ta ce marigayin ya yi kasa a gwiwa, amma saboda takaita zirga-zirgar ababen hawa da aka yi wa tashar Total Radar Coverage of Nigeria (TRACON), ba a garzaya da shi asibiti ba.
“Kafin su sami abun hawan da za su garzaya da shi asibitin ne kuma ya ce ga garuku nan,” in ji majiyar.
Marigayin jami’in hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya NAMA ne.
Majiyar ta ce, “Ina so in yi kira ga hukuma musamman mazabar sa ta NAMA, babban minista da kuma DG na NCAA da su taimaka wa iyalansa cikin gaggawa tare da fatan za a biya shi diyya mai kyau don karfafawa wasu gwiwa.
“Yayin da ake yin wadannan duka, ina roƙon a sake duba dokar hana ababen hawa zuwa wurin TRACON sannan a yi gwajin damuwa a kan waɗanda suka tsira.
“Ina mika wuya kuma ina neman addu’ar Ubangiji ya gafarta masa kurakuransa, kuma ya karba masa a kirjinsa.”
Daily trust ta ruwaito cewa wani ATC ya mutu kimanin makonni biyu da suka gabata, wanda ya zama manyan ma’aikatan NAMA guda biyu su rasu tsakanin makonni biyu.
Marigayin na farko, Mista Francis Anwetin, manajan gudanarwa na ATC a filin jirgin saman Asaba, wata mota ce ta same shi a dab da wajen kasuwanci.