Wani jami’in Dan sanda mai suna Sajan Adegoke Ogunsola ya mutu a gidan tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Ya bayyana cewa, Ogunsola na aiki ne a gidan Daniel, wanda aka fi sani da Asoludero, a garin Sagamu a karamar hukumar Sagamu ta jihar.
Da yake bayyana lamarin wanda ya faru a ranar Asabar din da ta gabata, Oyeyemi ya bayyana mutuwar dan sandan a matsayin hadari da ka iya faruwa ga kowa.
A cewarsa, dan sandan yana kokarin bude kofar gidan ne kafin daga bisani ya yanke Jiki ya fadi
Kakakin rundunar ya ce an garzaya da sajan zuwa wani asibiti amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
Daniel yayi gwamnan jihar Ogun a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Comments 1