• Jami’in ya kai harin ne a rukununin gidaje Golf Estate na jihar Enugu.
• Kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin Wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutun 5.
•Mr Aliyu ya ce, an kama jami’in dan sandan kuma a na cigaba da gudanar da bincike.
Rundunar yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da mutuwar mutun 5 a rukunin gidaje na Golf Estate, bayan wani jami’in dake aiki a wani kamfanin ya fita haiyacin shi, kuma ya farmaki yanki.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, mutun 4 sun sami mummunan raunuka, sanadiyar harin da aka kai da misalin karfe 9:30 na safe.
Kwamishinan yan sandan jihar Muhamad Aliyu ne ya tabbatar da faruwan lamarin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Daniel Ndukwe.
Mr Aliyu ya ce, an kama jami’in dan sandan, kuma a na cigaba da gudanar da bincike akan sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya gana da Ngige kan rikicin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna
Kazalika kwamishinan ya bai wa mataimakin shi, dake kula da sashin binciken manyan laifuka a jihar, da ya gudanar da cikakken bincike kan musabbabin faruwan harbe harben.
Lamarin da ya faru tare da wani Insfecta, dake aiki a karkashin rundunar bada Kariya ta musamman a Base 9, na garin Umuahia a jihar Abia, na aiki ne a wani kamfanin dake cikin gukunin gidaje na Golf Estate.
Sai dai kwamishinan ya kuma ce, mutun 4 da su ka sami raunuka an kai su asibiti, domin cigaba da kula da lafiyar su.
Inda kuma, “Mutun 5 daga cikin wadanda su ka sami munanan raunuka an tabbatar da mutuwar su, inji likitan dake aiki a asibitin” kamar yadda sanarwar rundunar yan sandan ta bayyana.