A yayin da ake fuskantar matsalar rashi aikin yi a Nijeriya musamman a tsakanin matasa, wani Kamfani mallakan kasar Japan a Nijeriya zai hada hannu da wani Kamfani a Nijeriya domin horas da matasa dubu daya.
A kwanan nan Hukumar tsaro ta NSCDC ta fitar da cewa mutane sama da miliyan 2 ne suke neman gurbin aikin mutum dubu 5 a hukumar a wani mataki da hukumar za ta dauki sabbin jami’ai.
Canon, shahrarren kamfanin kasar Japan, ya kulla yarjejeniya da kamfanin KAS da ke da kwarewa a fagen dab’i a Nijeriya, don fara amfani da na’urar dab’i irinta ta farko a wata kasa ta nahiyar Afirka.
Samar da wannan na’ura, dai ya sa ita ma gwamnatin Nijeriyar kulla yarjejeniya da kamfanin na KAS domin horas da matasa fiye da dubu.