By Abbas Yakubu Yaura
Wani kansila a karamar hukumar Funakaye dake jihar Gombe ya nada mutane 18 a matsayin mataimakansa domin su taimaka masa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
A wani nadi wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, dan majalisar, Yahaya A.G. Yusuf, mai wakiltar yankin Bajoga ta Gabas a karamar hukumar Funakaye, ya nada babban sakatare mai zaman kansa (PPS) da mataimaka na musamman 12 da kuma karin wasu mataimaka na musamman guda biyar.
Daga cikinsu akwai mataimaka na musamman kan harkokin siyasa, tallafawa marayu, shari’a da tsaro, yarjejeniya, harkokin mata da mataimaka na musamman kan harkokin addinin Musulunci da na Kirista, da kuma PA kan karbar korafin jama’a da PA kan nakasassu da masu fama da matsalar Jiki da dai sauransu. .
A wata tattaunawa ta wayar tarho da kansilan yayi da jaridar Aminiya ta Arewa maso Gabas, ya tabbatar da nadin, inda ya ce an yi hakan ne don yi wa al’ummarsa hidima sosai a matsayinsa na wakilinsu a karamar hukumar.
Ya ce ya riga ya zama hamshakin dan kasuwa lokacin da ya shiga siyasa, inda ya kara da cewa ya nemi kujerar kansila don yin hidima da kuma yin tasiri mai kyau ga rayuwar mutanen mazabarsa.
“Ba wai ina da arziki ba, amma albashina da alawus-alawuna sun isa in daidaita albashin mutanen da na nada a kowane wata saboda na shiga siyasa don taba rayuwar mutane ba don tara dukiya ba,” inji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Yusuf ya kuma gyara wani bangare na wata hanya a yankinsa, baya ga shirin bayar da tallafin karatu ga daliban firamare da sakandare da manyan makarantu na karamar hukumar Funakaye.
“Na riga na dauki nauyin dalibai 40 a karkashin gidauniyata, inda nake bayar da tallafin karatu ga dalibai 20 daga Firamare 3 – 6 da 20 na Sakandare na SS I – SS III.
Sannan ” baya ga dalibai uku na manyan makarantu a nan Bajoga,” in ji shi.
Kansilan mai shekaru 40 da haifuwa yayi karatunsa a fannin ilimin zamantakewa da ya kammala karatun digirinsa na farko a jami’ar Maiduguri, shi ne shugaban kungiyar ‘yan majalisar kansilolin Gombe a halin yanzu, kungiyar kansiloli daga unguwanni 114 na jihar.
A baya ya taba zama mataimaki na musamman ga tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo.