By Abbas Yakubu Yaura
Wani Kansilan mai wakiltar mazabu 5 a karamar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta Hon.Jude Adjekpogu, wanda ake zargin Fulani makiyaya ne suka harbe shi a kwanakin baya ya mutu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kansilan ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis a garin Warri inda yake jinya a wani asibiti mai zaman kansa da ba a bayyana ba.Idan dai ba a manta ba wasu da ake zargin makiyaya ne suka harbi kansilan mai ci a ranar Asabar 4 ga watan Disamba, 2021 a kan hanyar Eku zuwa Abraka a lokacin da yake dawowa daga bakin aiki.
Tun lokacin daya ke kwance a gadon asibitin ake ta faman ceto rayuwarsa sakamakon raunin daya samu a harin.
An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen da aka ce makiyaya ne sun tare hanyar Eku zuwa Abraka da misalin karfe 5:30 na yammacin wannan rana inda suka bude wuta kan motar kansilan inda harsasan suka same shi a cikinsa.
A saboda haka mazauna yankin sun yi kira ga karamar hukumar da gwamnatin jihar Delta dasu gaggauta kai dauki ga hare-haren da wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne ke kaiwa a hanyar Eku-Abraka.
Hanyar Abraka zuwa Eku a ‘yan kwanakin nan ta zama ruwan dare ga matafiya yayin da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami ke farautar matafiya a kullum.
A halin yanzu, shugaban karamar hukumar, Hon. Victor Ofobrukueta ya bayar da tabbacin cewa kungiyar masu tayar da kayar baya a yankin suna sa ido sosai kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar dasu gaban kuliya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ba’a samun damar jin ta bakin saba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.