Hukumar farin kaya ta Civil Defense ta bayyanawa cewa ta kama wani matashin direban babur mai kafa uku ɗan shekaru 25 a duniya da yayi yunkurin lalata wata yarinya mai shekaru 15 a yankin unguwar Brigade dake ƙaramar hukumar Nassarawa, a jihar Kano.
Shugaban hukumar na Kano Mista Abu Abdu je ya bayyanawa manema labarai a jiya Juma’a jim kadan bayan kama matashin.
Kamar yadda ya bayyana yace direban babur din mai suna Mansur Jibrin yayi kokarin jan hankalin yarinya wadda bakuwa ce tazo daga jihar Katsina.
Shugaban ya ce “direban yayi amfani da bakuntar yarinyar bayan ya dauko ta daga wajen Gidan Baban Gwari dake kan titin Katsina, inda yayi ta yawo da ita da sunan yana neman inda zai kaita har tsawon awanni biyar, daga bisani ya saya mata abinci domin ta ci, a wannan lokaci ne ta fuskanci abinda yake nufi kuma nan take ta ja hankalin wasu mutane dake gefe wanda suka sanarwa jami’an mu”.
Shugaban ya yi kira ga iyaye da ci gaba da sa ido akan inda yaransu suke zuwa da kuma halin da suke ciki, domin kaucewa fadawa mugun hannu, sannan ya sake kira ga jama’a da su ci gaba da bawa jami’an tsaro bayanai domin dakile ayyukan masu fyaɗe.