By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an cafke wani mai sayar da shayi mai suna Hamidu da laifin kashe wani kwastomonsa a Arepo dake karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa wanda lamarin ya rutsa dashi mai suna Musa, ya siyo kofin shayi a hannun Hamidu kuma ya biya shi naira 40 maimakon naira 50 akan yadda ake biya.
Hamidu kuwa a yunkurinsa na ganin an daidaita, sai ya shiga tashin hankali, wanda ya fara fada tsakanin mutanen biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya bugi Musa a kirjin sa yayin da wanda abin ya shafa ya fadi kasa.
Wani shugaban jam’iyyar Odua (Sabuwar Zamani) Olayiwola Ogunsolu, ya shaida wa wakilinmu cewa Musa ya mutu kafin ya samu wani taimako.
Ya ce, “A makon jiya Laraba muna a unguwar Arepo da ke karkashin gada sai muka ji hayaniya ta kaure a tsakanin al’ummar Hausawa da ke wurin.
“Da isa wurin, sai muka ga wani ya mutu, da muka tambayi abin da ya faru, sai aka ce mana mai sayar da shayin ya kashe shi ne saboda ya ki biyan naira 50 na kofi ruwan shayi daya. Nan take muka kira ofishin ’yan sanda na Warewa, lokacin da ‘yan sanda biyu suka zo daga ofishin, sai al’ummar Hausawa suka yi musu tirjiya.
“Mun kira DPO na ofishin ’yan sanda na Warewa, kuma ya aika da karin taimako. Daga baya ‘yan sanda sun tafi da wanda ake zargin.”
Wani dan uwan mamacin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an yi wa Musa naushi ne a kan Naira 10.
Ya ce, “Musa ya je siyan kofin ruwan shayi amma yana da naira 40 maimakon naira 50 akan yadda ake sayar da shayin. Hakan ya sa mai siyarwar ya fusata suka fara fada.
Mai shayin wanda ba a san shi ba a karkashin gadar a nan ko da yake wasu sun ce sunansa Hamidu, ya bugi Musa a kirji. Ya fadi ya mutu. Wasu mutanen mu ne suka shiga tsakani. ‘Yan sanda sun zo suka tafi da mai sayar da shayi.”
Shugaban al’ummar Hausawan yankin, Usman Shehu, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.
“Irin wannan lamari ba zai wuce ni a matsayina na shugaban al’ummar Arewa a wannan wuri ba,” ya kara da cewa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya yi alkawarin komawa ga wakilinmu.
Ya ce, “Zan kira DPO na ofishin ‘yan sanda na Warewa in don dawowa wurinku.”
Har yanzu Oyeyemi bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.