- Wani mutum da ya tafi Dubai, bayan da ya dawo sai ya tarar matarsa ta sami ciki wanda mai gadin gidan ya yi mata
- A halin yanzu matar tana ɗauke da ciki wata biyar, kuma mutane sun roƙi mijin matar da ya yafe mata amma ya rabu da ita.
- Labarin da @Postsubman ya wallafa a Twitter ya ja hankalin masu amfani da shafin sada zumuntar na Twitter.
Bayan ya shafe watanni takwas a Dubai, wani mutum ya dawo ya gida sannan ya gano cewa matarsa tana ɗauke da ciki na mai gadin sa.
A cikin wani labari mai tada hankali da aka aika a asirce zuwa @Postsubman, mutumin ya ce yana neman shawara kan yadda zai tafiyar da lamarin.
Mutumin ya ce a halin yanzu matarsa tana ɗauke da ciki wata biyar, kuma jaririn ba nasa ba ne saboda ya yi tafiya a birnin Dubai na kasar UAE
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Ɗan Najeriya Ya Ƙirƙiri Wata Motar Lantarki Mai Kama Da Babur Mai Ƙafa Huɗu.
Ya bayyana cewa mutane suna roƙonsa da ya yafewa matarsa kuma ya karbe ta, amma yana cikin wahala.
Mutumin ya ba da labarin cewa duk lokacin da ya ga matarsa da ciki, sai ya yi tunanin mai gadinsa da cin amana.
Ya rubuta: “Yayi wata 8 a Dubai sai ya gano matarsa ta riga ta kwana da mai gadinsa, har tana da ciki wata 5, ban taɓa yaudararta ba duk da jarrabawar da nake fuskanta kullum.”
Martani daga masu amfani da shafin Twitter kan wannan lamarin!
@Ikechukwuisking ya ce: “Ka yafe mata ka ɗauki yaron a matsayin naka, ka sa komai a hannun Allah, za ta chanza ta yi maka hidimar miyar ganye mai daɗi, kar ka sake ta oh.”
@excelsiocarus yayi sharhi: “Lmao wace shawara kake nema? Ka riga ka san me kake son yi kana neman ra’ayi na biyu wanda ya goyi bayan shawararki.”
@delta_last_BABY ta ce:”Ka bar auren ku ya cigaba da zama lafiya ina rokonka.”
Comments 1