By Abbas Yakubu Yaura
A yammacin Lahadin da ta gabata ne wani malami mai suna Ayatu Momoh a Kwalejin Fasaha ta Tarayya dake Offa a Jihar Kwara ya rasu yayin da yake tsaka da halartar wani taron al’umma.
Momoh,kafin rasuwar sa wanda ya kasance malami a Sashen Cibiyar koyar da aikin Jaridar na kwalejin, sannan kuma ya fito ne daga Jihar Kogi kuma shi ne sakataren karamar hukumar Igala a Offa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Yana halartar wani taron al’umma ne a lokacin da lamarin ya faru.
Duk da cewa shugaban sashen yada labarai na cibiyar koyar da aikin Jarida, Olayinka Iroye, bai amsa kiran da aka yi masa ta wayar tarho ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto a ranar Lahadi, sai dai wani malami a sashen ya tabbatar da mutuwar Momoh.
Malamin, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa wakilinmu cewa, “mun samu labarin ya fadi ne wanda bayan haka yace gagarinku nan a lokacin da yake halartar taron sa na kabilar Igala a Offa ranar Lahadi. Sannan kuma ya kasance sakataren al’ummar garin na Offa”.