Wata babbar Kotun Majistare da ke zamanta a Kafanchan a Jihar Kaduna ta tura wani matashi zuwa gidan kaso, saboda zargin satar yarinya ‘yar kimanin shekara 15 da ya yi.
Alkalin kotun Abdul’aziz Ibrahim ya ki aminta da hujojjin da matashin ya gabatar a gaban kotun, inda ya yi umarnin a tura shi zuwa gidan kaso sai ranar 8 ga watan Yuli domin sake sauraron ƙarar.
Mathias Joseph, mai shigar da kara daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna ya bayyana wa kotun tun da farko cewa an kawo rahoton ne ga Cibiyar Salama da ke sauraron koke-koken cin zarafin mata da kananan yara da ke garin Kafanchan inda daga nan aka tura batun zuwa ga Hukumar farin kaya ta Civil Defense (NCDC) don ci gaba da gudanar da bincike.
Joseph ya ce wanda ya kawo karar daga garin Jagindi Tasha yake a Karamar Hukumar Jama’a, inda ya yi zargin cewa wanda ake hutuma ya aiko da bukatar neman auren budurwar, amma suka ki amincewa da hakan, sannan shi da Mai Unguwarsu suka ja masa kunne da ya fita harkar ‘yarsu saboda rashin aminta da dabi’unsa.
Bayan gudanar da bincike bayan batar yarinyar, sai aka gano cewa matashin ne ya ɗauke ta zuwa wata maɓoya.