By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ekit ta gurfanar da wani mai suna Falana Ayomide mai shekaru 28 a gaban wata kotun majistare dake Ado-Ekiti bisa zargin satar wayar Techno 3LA da kudinta ya kai naira 47,500.
Dan sanda mai gabatar da kara Sajan Sodiq Adeniyi ya shaida wa kotun a jiya cewa, a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2021, da misalin karfe 1:00 na dare daura da titin kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya NTA, dake Ado-Ekiti, wanda ake zargin ya sace wayar Techno mallakar wani Bakare Temitope.
Sajan Adeniyi yace wayar na dauke ne da katin kira na naira 40,000 da kuma Data ta naira 10,000.
A cewar mai gabatar da kara, laifin da aka aikata ya sabawa sashe na 390 da 419 na kundin laifuffuka na C16,1 na jihar Ekiti na shekarar 2012.
Lauyan wanda ake kara, Barista M.O. Adefisayo, ya bukaci kotun data bayar da belin wanda yake karewa, kan cewa zai bi sharuddan belin.
Alkalin kotun, Misis Mojisola Salawu, ta bayar da belinsa a kan Naira 20,000 tare da tsayayyiyan wanda zai tsaya masa sannan ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Janairun 2022, don ambato.