By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan sanda a jihar Ondo sun damke wani matashi dan shekara 29 mai suna Paul Samuel bisa zargin kashe babban abokinsa, Haruna Shaibu kan sayar da babur dinsa.
An gano marigayin ya bace tun ranar 20 ga watan Disamba har zuwa lokacin da aka gano cewa wanda ake zargin ya kashe shi ne domin ya sayar da baburdin sa.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa babban yayan mamacin ya shaidawa ‘yan sanda cewa yana zargin Samuel ya yi amfani da abokin nasa ne wajen yin tsafin kudi dashi bayan ya bata.
Rahotanni sun bayyana cewa dan’uwan marigayin ya shaida wa jami’an ‘yan sanda cewa an ga dan’uwansa na karshe tare da wanda ake zargin kuma mahaifiyar wanda ake zargin ta kira shi cewa an ga dansa a garin Yara dake Jihar Kogi yana tattaunawa kan sayar da babur din da ake zargin na dan uwansa ne daya bace.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majiyar ‘yan sandan ta ce, lokacin da aka kama wanda ake zargin ya amsa laifin kashe abokinsa ne domin ya sayar da babur dinsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Oyeyemi Oyediran ya tabbatar da kama wanda ake zargi da kashe babban abokinsa kan sayar da babur dinsa.