Wani matashi dan shekara 25 mai suna Banji Adebayo ya rasa ransa a ranar Litinin bayan da ya fada cikin rijiyar gida a jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a yankin Ile-Nla na garin Omu-Aran, dake karamar hukumar Irepodun ta jihar.
An ruwaito cewa wanda abin ya shafa, wanda ya je diban ruwa ne, ya tsunduma cikin rijiyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya ce an tsinto gawar wanda aka mutumin tare da mikata ga iyalansa.
Ya ce, “Daraktan ma’aikatar, Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su yi taka tsantsan a harkokinsu na yau da kullum.”
A wani labarin kuma
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 4 da wasu mutum 5a Katsina
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi garkuwa da matan aure hudu da wasu biyar a Shema Quarters da ke karamar hukumar Dutsin-Ma a jihar Katsina yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.
Maharan da suke da yawa dauke da AK-47 da sauran makamai, rahotanni sun ce sun kai farmaki unguwar ne da misalin karfe 11:30 na daren Lahadi, inda suka yi ta ta’addanci kusan awanni uku kafin zuwan tawagar jami’an tsaro.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito daga mazauna unguwar cewa ‘yan bindigan sun dira gidan Usman Abdullahi Yarima inda suka yi awon gaba da matansa biyu tare da wasu mutanen gidansa guda uku sannan suka wuce gidan Abdulaziz Lawal suka tafi da matansa biyu da wasu ‘yan uwasa biyu.
Rahotanni sun ce maharan sun sha karfin mazajen, inda suka gudu domin tsira da rayukansu, inda suka bar mutanen gidansu a hannun ‘yan ta’addan.
Da yake tabbatar da rahoton, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce: “Eh, an sanar da ni harin amma a halin yanzu bayanin da nake da shi kadan ne, kuma zan dawo gare ku, idan na samu cikakken bayani.”
Isah, ya bayyana cewa, an riga an shirya motocin jami’an tsaro masu sulke na Dutsin-Ma tare da wasu jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, domin yin artabu da ‘yan ta’addan.
Ya kuma musanta zargin cewa maharan sun kwashe kusan sa’o’i uku a yankin suna cin karen su babu babbaka.
“Mun samu wannan rahoton da misalin karfe 11 na dare amma sun yi aiki har zuwa karfe 2 na safe, wanda ba zan iya cewa gaskiya ba ne,” in ji Isah.