By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani matashi dan shekara 32 mai suna Toheeb Akanji (a.k.a T.cash) bisa laifin kashe wani matashi mai suna Damilare Oladipupo mai shekaru 42 da haihuwa.
Oladipupo mamba ne na daya daga cikin kungiyoyin sufuri a jihar Ogun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
A cewar Oyeyemi, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan kiran da aka yi masa a hedikwatar reshen Agbado da misalin karfe 12:30 na dare daga wani Oluomo, cewa wani Oladipupo Babatunde (wanda aka fi sani da No story) wanda ya zo otal din Blue Roof dake Adiyan Gasline don tayar murna ga mai otal din, inda wani da ba a san ko wane ne ba ya daba masa wuka ya kashe shi har lahira.
“Bayan wannan kiran na gaggawa, DPO, reshen Agbado, CSP Kehinde Kuranga, ya tara mutanensa zuwa wurin dan gano ko meke faruwa, inda suka gano cewa an fizge mamacin daga otal din inda aka caka masa wuka da dama a kirji, hannu da fuska.
Sai dai tuni aka garzaya da marigayin asibiti inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, wanda a nan take ya sanar da cewa dole ne a farauto wanda ake zargin sannan a gurfanar da shi a gaban kotu cikin sa’o’i 24.
“Bayan umarnin CP, DPO da mutanensa sun fara gudanar da bincike na sirri, kuma da misalin karfe 5 na yamma. na ranar 25 ga watan Disamba 2021, an kama wanda ake zargin. A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kashe mamacin amma ya dora laifinsa kan aikin sharrin shaidan.
“Ya bayyana cewa ya zo otal din ne domin ya gano wadanda suka yi wa daya daga cikin yaran nasa duka har suka raunata shi, amma da isa wurin, marigayin ya tare shi ya fara fada da shi. Daga nan ne ya fito da wukar da ya zo da ita ya caka masa wukar.”
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa sashin binciken laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.