Wani matashi mai suna Bobby Gabriel ya kashe dan uwansa dattijo har lahira a unguwar Duburo da ke karamar hukumar Khana a jihar Rivers
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, wanda ake zargin na da kimanin shekarun ashirin ne, ya kashe dan uwansa Mai suna, Kopapa Neete wanda ya cika shekaru arba’in, yayin wata takaddama da ta barke a tsakanin su, a daren ranar Lahadi.
An tattaro cewa wanda ake zargin ya tsere daga cikin garin lokacin da ya lura dan uwan nasa da ya caka ma wuka, ya mutu.
Shugaban Kwamitin Ci gaban Al’umma na Duburo (CDC) Mista Vincent Gbosi, ya tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wayar tarho, sannan ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Bori.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu Tallafawa Nigeria Wurin yaki da Yan bindiga~ inji Amurika
Gbosi yayi kira ga gwamnatin jihar da ta shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin.
Ya ce: “A jiya akwai wani abu a cikin garin Duburo inda wani Bobby Gabriel ya cakawa wani dattijo mai suna Kopapa Neete wuka har lahira. Haƙiƙa ‘yan uwan juna ne.” Inji shi.
“A matsayinmu na al’umma, mun yi kokari don kai korafi ga rundunar yan sanda a sashin Bori” inji shi.
“Muna amfani da wannan hanyar don yin kira ga gwamnati da ta duba halin rashin tsaro a cikin al’umma,” in ji Gbosi.
A halin da ake ciki, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.
Comments 1