Wani matashi a jihar Adamawa ya amince cewa ya daba wa wani mutum wuka saboda mutumin ya haska mahaifiyarsa da fitila wato (filashin).
Matashin mai suna Garga Joggi a yanzu haka yana hannun hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa bisa laifin dabawa wani Umaru Sanda wuka wanda ya kai ga halaka shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: PSG: Babu Kocin Da Zai Buga Wasa Da Yan Wasa Uku A Tare – Riolo Ya Caccaki Messi, Neymar, Mbappe
An ce Garga Joggi dan shekara 20, wanda dan kabilar Waltadi ne, a karamar hukumar Song, ya yi sanadin mutuwar Umaru ne a ranar 20 ga watan nan, kamar yadda DAILY POST ta rawaito.
Ana zargin wanda ake zargin ya daba wa marigayin wuka ne saboda ya haska mahaifiyarsa da fitila irin salonnan na filashin da aka ce tana tare da wasu mata a lokacin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, wanda ya yi magana game da lamarin, ya tabbatar da cewa, hatsaniya ta kai ga amfani da wuka da wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar Umaru.
A cewar Nguroje, Joggi ya shaidawa ‘yan sanda cewa marigayin ne ya fara dukansa, kuma a nasa bangaren, ya yi amfani da wuka a hannunsa ya daba wa marigayin a baya.
Nguroje yace wanda ake zargin za a gurfanar da shi a gaban kotu a kan matakin da ya dauka.
A wani labarin kuma, Shugaban Tsaro Irabor Ya Hakurkurtar Da Tsofaffin Ma’aikatan Soji Kan Rashin Biyan Su Hakkokin Su
Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Lucky Irabor, ya roki jami’an soji da suka yi ritaya da su yi hakuri da Gwamnatin Tarayya a kokarinsu na biyansu alawus din Tsaro.
A cewarsa, wadanda suka yi ritaya kafin a fara aiwatar da dokar ba su cancanci a biya su alawus din ba, ya kara da cewa ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake duba dokar.