Wani matashi ya hallaka dalibai kananan yara bakwai yayin tare da wasu baligai biyu yain wani hari kunar bakin wake da ya wata makaranta a birnin Kazan na kasar Rasha.
Kazalika karin wasu mutane ashirin da daya sun jikkata wadanda galibin su kananan yara ne sakamakon harin matashin mai shekara 19.
Harin ya auku ne a daular Tatarstan mai nisan sama da kilomita 820 daga fadar gwamnatin kasar, Moscow.
Da yake Tsokaci dangane wannan muguwar Kaba’ira, shugaban Kasar Rasha Vladmir Putin ya ce zai kawo sauyi game da dokar mallakar bindiga.
Yanzu haka haren-haren bindiga na ci gaba da zama ruwan dare a kasar, kuma wanda ya faru a yan baya-bayan nan shine na yankin Crimea a shekarar 2018.