Wani matashi ya fito ya bayyana irin yadda amininsa ya jama sana’ar tuka Keke NAPEP duk da cewa yana da digiri har guda biyu.
Matashin da ya bayyana wannan lamari da aka bayyana sunsa da Paschal ya ce abokin nashi ya gaza samun wata mafita da ta wuce kama sana’ar tuka Keke NAPEP bayan da aikin gwamnati ya gagare shi, kawai sai ya yanke shawarar ajiye girman kai a gefe don talkafa wa rayuwar shi.
Ya ce ya kama sana’ar ce ma ba da kudinsa ba, domin sai da ya nemi lamunin kudi gabannin siyan Keke NAPEP din, saboda ya ce ba zai zauna ya zura idanu kawai ba shi da abun yi ba.
“Abokina ya gama masters din shi amma kuma ba aikin yi, shine ya yanke shawarar karɓar lamunin kudi don fara sana’ar tuka Keke NAPEP”
“Ya sayi Keke NAPEP din ne ma a ta yanar gizo, kuma gashi yanzu haka yana ta zama wani hamshaki ba tare da wani aune ba” cewar matashin.