Wani matashi mai shekaru 25 mai suna Ismail Saliu, Rundunar Jami’an tsaro na sibil difens sun damƙe shi, da laifin haɗa baki da wani mai magani da wani, inda suka kashe ɗan uwan sa a Jahar Kwara.
Mai magana da Rundunar Jami’an tsaro na sibil difens a Kwara Babawale Afolabi wanda ya bayyana haka a cikin wani jawabi daya fitar, a ranar Asabar a Ilorin, yace Saliu ya haɗa baki da wasu mutane biyu, inda suka kashe ɗan uwansa mai shekaru 14 mai suna Azeez Saliu, da manufar amfani dashi domin yin tsafi, don samun kuɗi.
Afolabi yace lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Satumba na Shekarar 2021 a Kosubosu dake ƙaramar hukumar Baruten ta jahar kwara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PDP ta lashe zaben Karamar hukumar Kajuru
“A ranar 13 ga watan Satumba, jami’an tsaron sibil difens a Kosubosu suka samu kira daga wani maƙwabcin shi, cewa akwai zirga-zirgar wasu mutane da ba’a gane ko su waye ba a yankin.
“Wasu daga cikin jami’an sun yi saurin kai ɗauki a yankin tare da samun nasarar kama wani Mai Saida maganin gargajiya Ahmed Nkwe mai shekaru 44, da Ismail Saliu mai shekaru 25 gami da Saliu Ahmed mai shekaru 30,” inji Afolabi.
Mai magana da yawun Rundunar yace bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun galabaitar dashi a gona, kafin daga bisani ɗan uwansa ya kashe shi da hannun sa wato Saliu.
Yace waɗanda ake zargin da mataimakan sa, an samu nasarar kama su akan hanyar su ta komawa gonar.
Afolabi yace dukkanin waɗanda ake zargin da ɗan uwansa sun tabbatar dacewa shi ya kashe ɗan uwansa da taimakon mai magani da wani kuma.
Yace kwamandan rundunar Ayinla Makinde an sanar dashi lamarin, kuma ya bada umarnin a miƙa waɗanda ake zargin ga ƴan sanda domin cigaba da bincike tare da zartar masu da hukunci.
Comments 2