Wani abin takaici ya faru a Kaduna yayin da wani matashi ya nutse a cikin wani kogi da ya ratsa ta cikin sabuwar unguwar Hayin Bello na jihar.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Asabar lokacin da matashin ya je bakin kogin don zubar da wasu tarkace.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Cikakkun bayanai na yadda ya fada cikin kogin ya kasance babu wanda ya sani, duk da haka, mazauna yankin sun taru a bakin kogin don kallon yadda masu ceto a cikin ruwan suka shiga cikin ruwa domin neman matashin.
Karanta kuma: Wani Matashi Ya Nitse A Teku Ya Yin da Yake Nunkaya
“An umarce shi da ya je ya zubar da wasu tarkace amma ya fada cikin kogin. Ba mu san yadda lamarin ya faru ba amma muna fatan samun gawarsa,” wani mazaunin garin ya shaida wa Daily trust.
An kuma tattaro cewa an dauko wasu takalman silifas guda biyu da ake kyautata zaton na wanda ya fada din ne a kogin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Hakimin kauyen Haying Bello, Alhaji Ibrahim Fagge, ya ce mamacin ya nutse a cikin wata unguwa da ke kusa da kogin, amma mutane sun shiga kogin da ke al’ummar Hayin Bello da fatan za a dauko gawar.
Ya kuma bukaci iyaye da su daina tura ‘ya’yansu kusa da kogin domin ba shi da tsaro.
A wani labarin kuma: Mahara Sun Yi Ajalin Mutum 4, Sun Kona Gidaje A Cikin Wasu Al’ummomi
Akalla mutane hudu ne rahotanni suka ce an kashe a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’umma biyu a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mazauna kauyen sun shaida wa jaridar Daily trust ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne tsakanin yammacin Juma’a zuwa safiyar Asabar.