Wani matashi ya tafka wata gagarumar aika-aika inda ya shiga har cikin masallatai yayi zamba cikin aminci.
Matashin mai suna Abba Haruna ya shiga hannun ƴan sanda bayan ya sace rufi da ƙofofin masallatai 14 a cikin ƙananan hukumomi uku a jihar Jigawa, da sunan zai gina musu sababbi.
Matashin da ake zargin dai ya shiga hannu ne bayan an gano cewa ɗan damfara ne. Ya cire dukkanin rufi da ƙofofin masallatan sannan ya sayar da su ga ƴan bola-bola.
KU KARANTA: Bayan kwashe shekaru 9 suna soyayya, budurwa ta biya sadakinta da kanta
Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa kakakin kotun majistare ta garin Kiyawa, Abbas Rufai Wangara, yace ana zargin Haruna da lalatawa haɗe da satar kwanon rufi, ƙofofi da tagogin masallatai.
Hakanan kuma BBC ta rahoto cewa wanda ake zargin yayi awon gaba da kayan masallatai 14 a ƙananan hukumomin Taura, Kiyawa da Jahun na jihar ta Jigawa.
Dagacin garin Kanoke, Ussaini Wanzam Ilyasu, ya gayawa ƴan jarida cewa Haruna ya zo ƙauyen na su wasu makonni da suka gabata, inda yace musu yana aiki da wata ƙungiyar larabawa mai zaman kanta wacce zata gina musu babban masallaci, domin haka sai su ruguza tsohon.
Haruna ya shiga hannu ne bayan an ganshi yana ƙoƙarin yaudarar wani ƙauyen inda jami’ai suka ankara bayan ganin alamun rashin gaskiya a tattare da shi.
Rashin Miji Na Damuna, Na ƙosa Nayi Aure -Kyakkyawar Budurwa Ta Koka
A wani labarin na da
ban kuma, wata kyakkyawar budurwa ta fito duniya ta nuna yadda matsalar rashin aure ke ci mata tuwo a ƙwarya.Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya ta koka a kafafen sada zumunta kan yadda har yanzu bata samu mijin aure ba.
Kyakkyawar budurwar wacce ke amfani da sunan Chris Amrah a manhajar TikTok, ta sanya wani bidiyo inda take cewa ta gaji matuƙa da zama babu miji sannan ta ƙosa tayi aure domin ta ji abinda ake ji a rayuwar aure