Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar da kama matashi nan wanda ya ce zai sayar da kan sa saboda talauci ya dame shi, bayan da bidiyon matashin yake cigaba da karade shafukan sada zumunta.
Babban Kwamandan hukumar Haruna Ibn Sina ta cikin wani sakon murya daya turowa jaridar Dimokuradiyya, ya tabbatar da kamen matashin mai kimanin shekaru 26, yana mai cewa abunda ya aikata haramun ne a addinin musulunci.
Aliyu Idris wanda tela ne, ya ce yana cikin matsalar kuɗi, don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan 20 sannan ya yi wa mutumin da ya yi alkawarin sayensa hidima da zuciya ɗaya.
To sai dai bayan da ya gurfana a gaban hukumar matashin ya godiyawa hukumar Hisbah, inda yace sun masa karamci sakamakon nasiha da suka yi masa kan haramcin abunda ya aikata.
‘’Naji dadi gaskiya da yadda hukumar ta yi mun nasiha da wa;azi, cewa abunda nake ya sabawa da addinin musulunci, dan haka na daina kuma zan cigaba da sana’ar da nake yi tun da fari.’’ A cewar matashin Aliyu