Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Musa Bello, ya gindaya sharudda ga Limamai a lokacin gudanar da Sallah domin takaita yaduwar cutar Covid-19 karo na uku. Jaridar Pmnews ta wallafa haka a shafinta
Wannan sanarwar ta fito ta hannun Sakataren sa Anthony Ogunleye.
KARANTA:- Har yanzu ni ne dan takarar Gwamnan Anambra a PDP, Cewar Valentine Ozigbo
Ministan ya sanya doka wajan gabatar da huduba kada tayi tsawo, sannan a kammala komi da komi a cikin awa daya.
Ya kara da cewa wajan gudanar da Sallah ya kasance an raba adadin masu shiga kashi biyu don samun tazara.
A yayin gabatar da bukukuwan Sallah a garin Abuja, yace duk wani gidan motsa jiki da na wasanni su kasance a kulle.
Duk a cikin bayanin nasa ya gargadi masu zuwa Sallah da su kasance sun sanya takunkumi suna bada tazara sannan da wanke hannu a koda yaushe.
A wani labarin
Sarkin Kano ya dakatar da Dagaci kan sayarma Fulani fili
Sarkin Karaye dake Jahar Kano ya sanar da dakatar da Abdullahi Sa’adu, Dagacin Kauyen Butu-Butu dake karamar hukumar Rimingado a Jahar Kano bisa laifin sayarwa Fulani fili. Jaridar the Cable ta ruwaito
Masarautar Karaye na daya daga cikin Masarautu hudu da gwamanan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samar a shekarar 2019.
Mai Martaba Ibrahim Abubakar shine Sarkin Karaye.
Haruna Muhammed Gundumawa, mai magana da yawun Masarautar shine ya bayar da sanarwar tsige Dagacin a ranar Juma’a.
Kamar yadda ya bayyana “Su dai fulanin sun zo sun fara gina Masallaci ba tare da bin ka’idar kauyen ba, wanda haka ya janyo rikici tsakanin su da mutanen Kauyen.”
“An dakatar da Dagacin ne domin samun damar isasshen bincken kan yadda lamarin ya auku.”
Shidai Hakimin Rimingado Auwal Ahmad Tukur (Magajin Rafin Karaye? ya rubutu takardar korafi zuwa ga Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar kan abunda Dagacin ya aikata.
Sarkin Karayen Ibrahim Abubakar ya tura Habibu Umar Madakin Shamaki, daya cigaba da Jagorantar Kauyen da bincike kan yadda lamarin ya auku.
Sarkin Karayen Ibrahim Abubakar yayi kira ga Mutanen Butu-Butu da su baiwa Habibu Umar hadin kai wajan jagoranci da kuma bincike.