By Ishaq Dabai
An kama wani mutum mai shekaru 44, mai suna lge Ayodele, wanda ya damfari masu neman aikin yi na miliyoyin naira, a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a Akure, kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya, Hammed Abodunrin, yace wanda ake zargin ya damfari mutane 19.Abodunrin ya kara da cewa, “Rundunar‘ yan sandan dake yaki da ta’addanci ta cafke wanda ake zargi a Okuta Elerinla, a cikin garin Akure saboda yawan korafe-korafen aka shigar daga wajen wadanda aka damfara.
Wanda ake zargin a wata hira da aka yi da shi ya shaida cewa yana da hanyar sadarwa na neman aiki tare da taimakon wani babban jami’in gwamnati.Ige yace ya tara kimanin naira miliyan biyu daga hannun wadanda abin ya shafa.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya tara naira miliyan 1.3 daga hannun wadanda abin ya shafa domin neman guraben aiki a hukumar NDLEA,da NSCDC da ayyukan koyarwa na tarayya bayan ya tattara takardun shaidar su, yace an tura kudin da aka karba daga garesu zuwa ga Mista Adu don samun ayyukan bogi ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa duk kokarin rundunar tayi na sasanta lamarin tsakanin wanda ake zargi da wadanda abin ya rutsa dasu ya ci tura, saboda wanda ake zargin ya sha yi wa wadanda abin ya rutsa da su barazana.bayan “Lokacin karewar binciken mu, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu saboda sabawa sashe na 112 na dokar aikata manyan laifuka ta shekarar 2006.
Abodunrin yace NSCDC a matsayin Hukumar Tsaro ta kyamaci duk wani aiki na aka samu ta hanyar riya da cin hancin aiki, jama’a da masu neman aikin da ba su da tabbas su guji ba da kudade ga ‘yan damfara don guje wa yaudarar su.