Wani mutum mai suna Abubakar Abubakar, ya harbe kaninsa, Yusuf Abubakar, mai shekaru 12, har lahira a lokacin da yake gwada ingancin wata sabuwar laya da aka sayo da ake tana hana harbin bindiga.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Abubakar tare da mamacin ‘ya’yan wani mafarauci ne a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Yankuna 12 A Jihar Edo
Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata kuma Rahotanni sun ce Abubakar ya tsere ne bayan ya aikata wannan aika-aika.
Da yake magana kan lamarin a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Paul Odama ya bayar da umarnin gudanar da bincike.
Okasanmi ya kara da cewa, “Bayan sun yi amfani da layar, babban dan ya dakko bindigar mahaifinsa inda ya harbe kaninsa, layar taki aiki kuma Yusuf ya mutu nan take.”
Okasanmi ya shawarci iyaye da masu kula da su da su sanya ido kan ayyukan ‘ya’yansu.
“Ya kamata su guji yin wasu ayyukan da ba su dace ba don hana afkuwar wannan dabi’a a nan gaba,” in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Hukumar NDLEA Ta Kama Tsohon Dan Kwallon Najeriya Da Hodar Ibilis
Jami’an hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wani tsohon dan wasan kwallon kafa, Okafor Emmanuel Junior a filin sauka da tashin jirgin saman Murtala Muhammed da ke dauke da hodar ibilis mai nauyin kilo 1.40 a boye a cikin jakunkunansa.
Channels TV ta ruwaito cewa, An kama matashin mai shekaru 33 a ranar Litinin bayan ya taso daga Sao Paulo na Brazil inda ya biyi ta Adis Ababa, a cikin wani jirgin saman kasar Habasha, bayan da jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi suka gano cewa ya boye haramtattun kayayyaki a cikin jakunkunansa.