An tsinci gawar wani mutum da mace a cikin wata mota ƙirar sienna a iyakar Mowe/Ibafo na Babbar Hanyar Lagos zuwa Ibadan a ranar Laraba.
Wakilin majiyar mu ya tattara cewa, mazauna yankin sun ce sun ga mota a ranar Talata, kulle da mutane guda biyu masu ita.
A cewar wanda ya shaida lamarin, Motar mai Lamba LSD 992 HH, ta ɗauki kwanaki uku a wurin, kafin mutane su gano cewa, masu ita sun mutu.
KARANTA WANNAN LABARIN: NAHCON ta umarci hukumomin alhazai na jihohi dasu fara shiri domin Hajjin 2022
Amma akwai ruɗani akan musabbabin mutuwar mutanen dake cikin motar.
Wani mazaunin yankin da ake kira da suna Jane yace, ” motar ta daɗe tun ranar Litinin. Amma da safen nan, mutane sun je wurin, tare da gano cewa akwai gawar mutane biyu. Amma bamu san miya kashe su ba.”
Wata Majiyar tace, ƙila mutanen biyu, sun sadu ne da juna a lokacin da lamarin ya faru.
“Mun gano cewa, mutanen guda biyu sun sadu ne da juna a cikin motar, amma sun mutu kusa da wajen wani wurin bauta na Nafsat,” inji Majiyar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da lamarin, inda yace lamarin kodai kisa ne, ko kashe kai.
Oyeyemi yace dukkanin su basu mutu ba a lokacin da suke saduwar a cikin motar, yace abin zai iya kasancewa mutuwa ko kisan kai.
“Basu mutu ba a lokacin da suke saduwa. Abun da ya faru shine yarinyar ta kasance budurwar sa ce. Ya karɓar mata hayar wani gida a Lagos. Yaje ya ziyarce ta. Bamu san abinda ya faru tsakanin su ba, amma ya buge ta a kai, inda ta faɗi ta mutu.
“Ya ɗauki gawar ta a cikin motar shi. Al’ummar yankin sun ruga wajen ƴan sanda domin su kai rahoto. Sai ya nufi gidan sa dake Orimerunmu. Ya Ajiye wata takarda yana sanar da matar shi cewa ya kashe wata. Ya gayawa matar shi kada ta damu da neman sa, yana mai umartar ta data kula da ɗiyan su. Daga nan yabar gidan.
“Ya tuƙa motar inda ya tsaya kusa da wajen ibada na Nasfat, daganan ya kashe kansa, inda aka ga yasha guda ne. Ya faffasa gilasan motar, to wannan lamari ne na kisa da kashe kai,” inji Oyeyemi.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan yace an kai gawar sa zuwa wurin ajiye gawa.