By Abbas Yakubu Yaura
Wani mai aski dan shekaru 23 mai suna Victor Akinwa, zai shafe wani lokaci a gidan yari bisa zarginsa da yin amfani da wata karamar tabarya wajen kashe mahaifinsa.
Wata Kotun Majistare da ke Akure a Jihar Ondo ta bayar da umarnin tsare shi.
An ce Akinwa ya aikata laifin ne da misalin karfe 1:30 na ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 2021 a titin Basic, Idanre a gundumar Majistare ta jihar Ondo.
Dan sanda mai shigar da kara, Obadasa Ajiboye, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya bugi mahaifinsa, Justus Akinwa, da wata karamar tabarya a ka, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.
Ajiboye ya ce laifin ya ci karo da sashe na 316 da 319 na kundin laifuffuka, 37, 1 na Dokokin Jihar Ondo shekarar 2006.
Duk da haka, ba a karɓi roƙon wanda ake tuhuma ba.
Ajiboye a cikin takardar neman baka ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali har sai an saurari shawara daga Daraktan kararrakin jama’a (DPP) na jihar.
Alkalin kotun, Damilola Sekoni, ya tasa keyar wanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali na Olokuta tare da dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2022.