Wani mutum ya rasa ransa yayin da mutane bakwai suka jikkata sakamakon wa i hatsari daya afku a yankin Alapere dake jihar Legas.
Lamarin dai ya auku ne yau Asabar, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta tabbatar.
A cewar hukumar babban sakataren Hukumar LASEMA Dr. Olufemi Oke Osaniyolu hatsarin tsakanin motar dakon kaya kirar J5 da wata Tirela wadda suka taho mun gama da juna.
Ya ce tuni dai suka kai wadanda abun ya rutsa da su zuwa asibiti yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan wanda ya rasa ransa.
A karshe ya shawarci al’umma kan su kasance masu tuki cikin nutsuwa da kuma kaucewa Aron hannu saboda yawancin abinda ke faruwa na daga hatsari ya kasance Aron hannu ne kan taimaka wajen afkuwar sa.