Wani Mutum a Kasuwar Ndalat, Nandi County na Kenya ya Kashe Matar shi da Ɗiyan sa guda 3, bayan haka, daga bisani ya miƙa kanshi ga Ofishin Ƴan Sanda na Kipkaren.
A cewar gidan Talabijin na NTV, lamarin ya faru ne a ranar Laraba da daddare, biyo bayan faɗa tsakanin Ma’auratan.
Philip Lokuruen Mai shekaru 40, ya tabbatar da aikata lamarin ga ƴan sanda, cewa ya kashe Matar shi Rispa Chelimo mai shekaru 25, da ɗiyansa guda uku Ian Kipkosgei Mai shekaru 11 da Brenda Mai shekaru 9 da kuma Linus Mai shekaru Linus Kipkosgei Mai shekaru 7.
KARANTA WANNAN LABARIN: Allah Daya Gari Banban: Ɗan Shekara 25 Zai Angance Da Masoyiyar Sa Mai Shekaru 85 A Duniya
Wata Kafar Sadarwa ta raba rahoton cewa yankin Nandi, Eunice Luley itace mutum ta farko data shaida lamarin a ranar Laraba.
Tace ƴan sanda sun ɗauki gawar mutumen zuwa wajen ajiye gawa domin yin bincike.
Duk da ba’a sanar da cikakken bayanin abinda ya haddasa faɗan ba, tuni ƴan sanda sun fara bincike akan mummunan lamarin, wanda ya sanya mutanen garin suke cikin halin damuwa.
Comments 1