• Wani mutun mai shekara 40 ya yi wa wata mata fyade yar shekara 60.
• Yaron matar ne ya kai karan mutun wurin jami’an yan sandan jihar.
• Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ya ce, mutumin ya yi kalaman da suka nuna ya aikata laifin.
Jami’an yan sandan a jihar Ogun sun kama wani mutun mai shekara 40 da zargin yi wa wata mata yar shekara 60 fyade.
Jimi’an dai, sun yi nasaran kama wanda ake zargin ne mai suna Adesina Ade, a ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2021.
A na zargin shi ne, da tirsasa wa matar wacce a ka sakaye sunan ta, yin amfani da ita.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Abimbola Oyeyimi ya ce, an kama wanda ake zargin ne, biyo bayan rahoton da yaron matar, ya shigar a ofishin yan sandan dake Idanyi, “inda ya ce, “Da musalin karfe 4 na yammaci ne, lokacin mahaifiyar sa tana gida, wanda ake zargin ya kutsa cikin gidan, inda a nan ne ya yi ma ta fyade” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe wani mutun bayan ya cire kudi a ATM
Ya kara da cewa, rahoton ne yasa jami’in dan sandan dake kula da yankin na Idanyi, ya baza jami’an yan sanda, domin kama wanda ake zargin.
“Kuma Jami’an sun yi nasarar kama shi, inda a kayi gaggawar kai matar asibiti, domin duba lafiyar ta”inji Oyeyimi.
“A karshe wanda ake zargin ya yi kalaman da suka tabbatar da cewa, ya aikata laifin” inji shi.
Comments 1