Shugaban kwamitin kula da harkokin yan sanda na majalisar dattawan kasar nan Sanata Halliru Jika, ya fice daga jam’iyyar APC.
Sanata Halliru ya kasance sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, kuma a zabe shi ne a jam’iyyar APC wadda yanzu ta zama tarihi a wajensa.
Kazalika ya kasance tsohon dan takarar gwamna a jihar, wanda yazo na biyu da kuri’a 278, a zaben fidda gwani da aka gudanar, wanda kuma tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya Abubakar Sadiq ya lashe da kuri’a 370.
Sanatan dai ya sanar da ajiye shahadar APC ne a wata wasika da ya aikewa da shugaban jam’iyyar Kafin Mafarki Dake karamar hukumar Ganjuwa.
Ficewar tasa na zuwa ne jin kadan da shima tsohon mataimakin gwamnan jihar Audu Katagum ya fice daga jam’iyyar ta APC.
An dai rantsar da Katagum matsayin mataimakin gwamnan tare da gwamnan Muhammad Abubakar, wanda shine ya baiwa na yanzu bayan yayi nasara.