Shugaban Karamar Hukumar Bogoro dake Jihar Bauchi Iliya Habila ya dakatar da Sarkin Kauyen Sabon Layi dake karamar, bisa zargin sa da lakada wa matarsa duka har ta ce ga garin ku.
A Jiya Lahadi ne Iliya Habila ya sanar sa daukar wannan mataki bayan gudanar da dogon bincike.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Gudanar da Mulki da ayyuka na karamar hukumar ya fitar, ta ce dakatarwa ta fara aiki ne nan take ba tare da wata-wata ba, har sai yadda binciken yan sanda na gaba ya bayyana.
“Shugaban Karamar Hukumar Bogoro dake Jihar Bauchi, ya dakatar da Sarkin Sabon Layi Kwara ASP Daniel Salka Mai ritaya bisa zargin Jibgar matarsa mai suna Hajara har ya aikata lahira”
“Ana zargin Mista Salka ne da wannan muguwar Kaba’ira tun ranar 19 ga watan Afirelun da ya gabata” Cewar Sanarwar.
Wakilin Mu a Bauchi Bashir Khalid Furyam wanda ya ga sanarwar ya labarto mana cewa, tun a ranar 26 ga watan Afirelun ne Jami’an tsaro na Bijilanti d kuma DSS suka yi ram da tsohon dan sandar a Kauyen Bayara inda suka damka shi wa rundunar yan sandar karamar Hukumar Bogoro don gudanar da bincike.