Wani Kofur a rundunar sojin Najeriya, Abayomi Ebun, ya murkushe Babban Daraktan kudi a cibiyar dake kula da sauyawa sojojin Najeriya wuraren aiki NAFRC, A. O James, da motarsa a jihar Legas. Kamar yadda Daily Nagerian Ta Ruwaito.
PRNigeria ta labartocewa lamarin ya faru ne a lokacin da Mista Ebun, wanda ke aiki a cibiyar samar da albarkatu ta Najeriya, NARC, ke tukin motarsa zuwa tsohon barikin NAFRC da ke Legas.
KARANTA WANANN LABARIN: Atiku Abubakar Ya Gana Da Kungiyar Editoci Ta Najeriya
Daraktan kudi na NAFRC, kamar yadda PRNigeria nakalto, an ce yana tafiya gidansa da ke cikin Barrack, sai motar sojan ta buge shi ta baya.
Nan da nan bayan faruwar lamarin, an yi gaggawar kwashe babban jami’in zuwa cibiyar kula da lafiya ta barikin NAFRC inda likitocin cibiyar suka tabbatar da rasuwarsa.
Wata majiya a Barikin ta NAFRC ta shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa Mista Ebun ya bugu ne da barasa a lokacin da lamarin ya faru kuma yana tukin ganganci.
“Hukumomin barikin na NAFRC sun tsare shi don ci gaba da bincike,” in ji majiyar.
A WANI LABARIN KUMA: Majalissar Wakilai Ta Dage Zamanta Na Gobe, Ta Sanya Sabuwar Rana
Majalisar wakilai ta dage ci gaba da zaman majalisar zuwa ranar Talata 22 ga watan Nuwamba, domin ba da damar yin wasu gyare gyare a zauren majalisar.
Magatakardar majalisar, Dakta Yahaya Danzaria ne ya sanar da dage zaman a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja