Wani tsohon ‘dan wasan baya na tawagar kwallon kafar kasar Faransa Jean-Pierre Adams ya rasu, ya na da shekaru 73 a duniya bayan ya kwashe shekaru kusan 40 a sume.
Adams wanda ya yiwa Faransa wasa a matakin kasa har sau 22 a shekarun 1970 ya suma ne, sakamakon wani kuskuren alurar da aka masa a shekarar 1982 lokacin da ake masa aiki a gwuiwar sa.
An haifi Adams a shekarar 1948 a Dakar dake kasar Senegal, kuma yana daya daga cikin ‘yan wasa na farko da aka haifa a wajen Faransa, da ya yiwa kasar wasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan kungiyar IPOB sun cinna wa Babbar Mota Wuta a Enugu
Kungiyar Nimes da ya yiwa wasa ta aike da sakon ta’aziya da ‘yan uwa da iyalan Adams.
Lokacin ganiyar wasan sa, Adams ya yiwa kungiyoyin Nice da Paris Saint-Germain wasa a gasar wasannin kasar na Faransa.
A wani labarin Kuma na daban.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon darakta Janar na shugaban hukumar kula da cutuka masu ya duwa NCDC Dakta Ifedayo Morayo Adetifa.
Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau litinin, Dakta Adetifa dai ya maye gurbin Dakta Chikwe Ihekweazu wanda a yanzu shine shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO a sahen cibiyar kula da annoba da fasaha wanda take a birnin Berlin na kasar Germany.
Kamar yadda ya wallafa a shafin makarantar kiwon lafiya dake birnin London, Dakta Adetifa yace “ya karbi kwalin digirin sa farko a jami’ar Ilorin dake jihar Kwara a kan harkar likitanci, sannan ya kammala karbar horo a asibitin koyarwa na Idi-Arabi dake jihar Legas.
“Kazalika nayi karatun digri na biyu MSc a fannin ilimin cututtuka sannan natafi zuwa karatun digri na uku PhD a dai fannini ilimin cututtuka a jami’ar Amsterdam dake Netherlands.