Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ki amsa gayyatar da Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki kasa zagon kasa (EFCC) ta yi masa kan wani bincike da ya shafi karkatar da kudade.
Daily Post taga wata takardar gayyata mai dauke da kwanan wata 12 ga watan Mayu 2023, wacce EFCC ta aika wa Fayemi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dubu ta Cika, Jami’an EFCC Sun Sake Kama Mompha
A cewar wasikar, Hukumar ta ce tana bukatar karin haske daga Fayemi a wani bangare na binciken.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a yi ganawar Fayemi da EFCC a ranar 18 ga watan Mayun 2023.
Sai dai Fayemi wanda ya amince da karbar wasikar hukumar ta hannun wakilansa na shari’a ya yi ikirarin cewa ba zai halarci tattaunawar ba a wannan rana ta musamman.
Tsohon Ministan ma’adanai na kasa ya bayyana cewa zai tsunduma cikin gabatar da wasu sabbin littattafai guda biyu don karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wani labarin kuma, NDLEA Ta Kame Wasu Mutane 85 Da Ake Zargin Dillalan Muggan Kwayoyi Ne a Kano
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano, a ranar Talata ta ce ta kama mutane akalla 85 da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne a wani kulob a jihar.
Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kama mutanen ne bayan wani samame da suka kai a wani kulob na Bubles da ke Kano wanda aka ce an mayar da shi wurin hada-hadar maggun kwayoyi.