Wasu rahotanni sun bayyana cewa rikici ya barke tsakanin wasu ‘yan uwa biyu ranar Talata a Okpunoeze, Uruagu, kan katse wutar lantarkin.
Al’ummar yankin sun tattaro cewa an samu matsala ne a lokacin da wanda ake zargin ya kasa biyan kudinsa na wata ₦1500, lamarin da ya kai ga katse hasken wutar lantarkin gidan sa, kafin ya fuskanci babban dan uwansa (da suke zaune a gida daya tare dashi).
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Zamu Taimaka Wajan Ganin PDP Ta Sha Kaye A Zaben 2023 —Martanin Wike Ga Ayu
Wata majiya ta ce: “Rikicin ya kai ga har Peter ya fusata, ya garzaya dakinsa, ya dauki bindigarsa, ya fito ya bindige babban yayansa, Godwin Orji.”
“Peter, bayan ya aikata wannan aika-aika, da sauri ya garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ya mika kansa, saboda tsoron kada a yi masa zanga-zanga.”
“Kafin wannan batu na baya-bayan nan, an dade ana takun saka tsakanin Mista Peter Orji da (Marigayin) kan wata takaddamar fili, wadda a dalilinta ya rika yin barazanar rayuwa ga babban yayansa, wanda hakan ya kasance ba a ɗauke shi da muhimmanci ba.”
Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama wanda ake zargin sabanin ikirarin da ya yi cewa ya mika kansa ga ‘yan sanda.
Ya ce: “An fara damke matar wanda ake zargin ne a wurin da laifin ya faru, bayan an kama shi da kansa; dukkansu a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda.”
“Kwamishanan ‘yan sanda, Echeng Echeng ya ba da umarnin a mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) domin gudanar da cikakken bincike na gaskiya.”
A wani labarin kuma, Yajin Aikin ASUU Ya Shafi Lafiyar Hankali Dalibai – Shugaban Jami’a
Shugaban jami’ar jihar Benue BSU dake Makurdi, Farfesa Joe Iorapuu, ya bayyana cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga na tsawon watanni shida a fadin kasar nan, tuni ya yi illa ga kwakwalwar dalibai.
Iorapuu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wasu ‘yan jarida a Makurdi a ranar Alhamis kan makomar daliban da suka kammala karatun digiri bayan yajin aikin ASUU da aka tsawaita.