Wannan Kashe-kashen duk yunƙuri ne na hana Ƴan Kudu Siyasa a matakin Tarayya — Inji Ehilebo na PDP
Shugaban Kafafen Sadarwa na Zamani na Jam’iyyar PDP Anthony Ehilebo tayi Allah wadai da harin ƴan bindiga a Jirgin Ƙasa tsakanin Katari da Rijani akan hanyar Abuja-Kaduna.
Ehilebo ya bayyana ra’ayinsa a matsayin wani yunƙuri na hana ƴan siyasar Kudu shiga harkokin Siyasa na Ƙasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗan Takarar Gwamnan Osun ya fice daga PDP, bayan yasha Ƙasa
Dayake Jawabi da Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya Fitaccen Lauyan dake Abuja yace Ƴan Siyasar Kudu bazasu iya baiwa Sojoji Umarni su magance matsalolin ƴan bindiga daɗi ba.
Ɗan Takarar Ɗan Majalissar Dokoki ta Edo yace Ƴan Siyasa Kudu za’a zarge su da yunƙurin kisan ƙare dangi idan sukayi kira ga Sojoji dasu kawo Ƙarshen Ƴan ta’adda.
A cewar Ehilebo “ina jin cewa wannan harin wani yunƙuri ne na korar ƴan siyasa kudu daga shiga Harkokin Siyasa a matakin Tarayya, domin babu wanda zaiso ya gaji wannnan matsala.
“Ɗan Siyasar Kudu bazai iya bada umarni ga Rundunar Soji ko ta Ƴan Sanda su kawo karshen ƴan bindiga, babu wanda zai iya, idan ma ya gwada, zasu cire yana Son kisan ƙare dangi.