Shugabannin Yankin Asiya sun yi kira ga kakkausar murya ga shugaban sojin Kasar Myanmar da ya dakatar da kisan da ake yi wa musulmin kasar.
Wannan ne karon farko da Jagoran Sojin Myanmar din Janar Min Aung Hlaing ya fita wani balaguro tun bayan juyin mulkin da ya yi a kasar a watan Fabrairu.
Sama da mutane 700 ne suka rasa rayukansu tun bayan juyin mulkin na watan Fabrairu inda kuma aka garkame masu zanga-zanga da yan siyasa da dama a ƙasar.
Duk da dambarwar da ake kan mummunar annobar nan ta Korona, amma hakan bai hana shugabannin kasashe 10 dake cikin Ƙungiyar Kasashen Asiya ba don tattauna matsalar a birnin Jakarta na Indonesiya.
Kuma wannan ganawa ta Jakarta ita ce irinta ta farko da aka yi don samo bakin zaren wannan matsaloli.
Firaministan Malesiya Muhyiddin Yassin ya bukaci da a gaggauta kawo karshen kashe-kashen da ake yiwa fararen hula a kasar ta Myanmar tare kuma da sakin yan siyasa da dama da ake tsare da su a gidan yari.
Kazalika shi ma Shugaban Kadar Indonesiya Joko Widodo ya kira kashe kashen da rashin imani, tare da gargadin Janar din sojin da ya sanya damba wa lamarin.