Wannan shine Jawabi na Ƙarshe na ranar Dimokuraɗiyya a matsayin Shugaban Ƙasar ku — Buhari ya tunatar da ƴan Najeriya
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shaidawa ƴan Najeriya cewa bazai ƙara yi masu jawabi ba, a matsayin Shugaban Ƙasa a ranar Dimokuraɗiyya.
Ya bayyana haka a cikin jawabin da ya yiwa Ƙasa a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dauda Lawal: Abubuwa 12 Game Da Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar PDP A Jihar Zamfara
A jawabin, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karanto wasu daga cikin ƙalubale da nasarorin Gwamnatin sa.
Ya bayyana gamsuwar sa da yanda aka gudanar da Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyu domin Babban Zaɓen Shekarar 2023, yana mai cewa Jam’iyyu sunyi abinda ya dace.
Yace Shugaban Ƙasa da zai gaje shi, zai kasance an zaɓe shi ne ta hanyar Zaɓe na Adalci, yana mai kira ga Ƴan Najeriya dasu fito suyi aikin su na ƴan Ƙasa.
“Yaku ƴan Najeriya, a yau itace ranar 12 ga watan yuni da muke bikin ranar Dimokuraɗiyya ta Ƙasa, wanda kuma muke murnar samun haɗin kan ƙasar mu.
“A shekarar 2018, mun matsar da ranar Dimokuraɗiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan yuni. Wannan canji ya tunatar da ƴan Najeriya gudanar da zaɓe na adalci.
Comments 1