By Abbas Yakubu Yaura
Wani mai shagon wanzanci mai suna Lucky Diri ya daba wa wani ma’aikacin babur mai suna Emeka Christian Udo mai shekaru 38 wuka da sukundireba sakamakon wata ‘yar rashin fahimta da ta faru a unguwar Sagbama da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa.
An ce wanda ake zargin ya samu sabani da marigayin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, kafin ya fito da wata sukundireba ya daba masa a haƙarƙarinsa na hagu.
A cewar majiyoyin al’umma, an kai marigayin babban asibitin Sagbama domin kula da lafiyarsa amma daga karshe ya rasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa jim kadan da faruwar lamarin, fusatattun matasan al’ummar sun kai gawar zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Sagbama kafin su koma shagon aski sai suka gano cewa wanda ake zargi da kisan kan ya tsere daga wurin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni jami’an tsaro na rundunar suka cafke mai aski, inda ya ce yana tsare a hannun ‘yan sanda a halin yanzu.
Sannan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nr Ben Nebolisa Okolo, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin, inda ya bayar da tabbacin za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
Ya ce: “Wannan abin takaici ya faru ne a ranar 06 ga watan Janairu, 2022, a unguwar Sagbama.
“Wani mai aski Lucky Diri ‘m’ mai shekaru 20, ana zarginsa da daba wa wani Emeka Christian Udo ‘m’ shekaru 38, wani mahaya babur sukindireba a hakarkarinsa na hagu, bisa wata ‘yar rashin fahimta.
“Nan da nan aka garzaya da wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Sagbama, inda ya mutu a lokacin da yake karbar kulawar likitoci.
“An kama wanda ake zargin, Lucky Diri, kuma an tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da yi masa tambayoyi,” in ji shi.