An kashe mutane 10 a wani mummunan hari da aka Kai a birnin New York na kasar Amurika. Wanda Kuma ake kyautata zaton cewa ramakon gayya ne ga laifin nuna kyama da ke da alaka da kabilanci.
An kama wani matashi mai shekara 18 sanye da kayan jami’an soji bayan an far bincike a wurin da lamarin ya faru a yankin Buffalo.
Wanda ake zargin ya shiga wani babban kanti ne da yammacin ranar Asabar kafin ya bude wuta. Inda ya yi amfani da na’urar daukar hoto wajen yada harin ta yanar gizo Kai tsaye, in ji ‘yan sanda.
Yayin da yake Mai da martanin kan Shugaban Amurka Joe Biden ya yi Allah wadai da abin da ya kira harin “abin kyama”.
“Muna binciken wannan lamarin a matsayin laifin nuna kyama da kuma wani lamari na tsatsauran ra’ayin wariyar launin fata,” in ji Stephen Belgia, wakilin ofishin FBI na Buffalo a wani taron manema labarai.
A wani labarin Kuma na daban
Zan gyara Najeriya cikin ƙanƙanin Lokaci — Inji Atiku
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP yace idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa na Najeriya, zai yi aiki tuƙuru da Ƴan Majalisu domin sake fasalin Najeriya.
Abubakar ya bayyana haka a ranar Asabar a Calabar a lokacin da yake jawabi da Wakilan Jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, a yayinda Jam’iyyar ta shirya gudanar da zaɓen fidda Gwani a ranakun 28 da 29 na wata Mayu.
Tsohon shugaban kasar yace zai bada gashin kai ga Jahohi da Ƙananan Hukumomi.
A cewar sa, za’a samu matsala idan har ba’a zaɓi nagartattun mutane a Shekarar 2023.
“Tarihi zai maimaita kanshi idan har masu kaɗa ƙuri’a basu zaɓi mutanen daya kamata su zaɓa domin su jagorance su.
“A shirye nake, na cancanta, ina dukkanin abinda ake buƙata, wanda shiyasa na bada kaina domin in Jagoranci Ƙasar.
“Ina da jajircewa na kawo gyara matsalar tsaro,” yana mai ƙara dacewa, Jam’iyyar PDP bazata taɓa amincewa ta kasance abokiyar hamayya ba.
Shima da yake jawabi a taron, Mr Liyel Imoke Tsohon Gwamnan Jahar Cross River, ya yabawa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar da irin namijin ƙoƙarin sa, yana mai cewa ya kasance waɗanda suka yanke wa PDP cibiya.
Imoke yace Atiku Abubakar shine wanda mutane suka zaɓa a Shekarar 2019 duk da bashi yaci zaɓe ba.
Yace PDP a Jahar Cross River ta Kasance iyali ɗaya, kuma zasu bada goyon baya a gareshi.
Idan dai za’a iya tunawa, Atiku Abubakar ya nemi Gwamnan Adamawa a Shekarar 1990 da 1997 zuwa 1998 kamin ya zama Abokin Takarar Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Shekarar 1999.