A daren yau za a fafata wasa mafi zafi a gasar zakarun turai wato wasan rukuni tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na ƙasar Italiya da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona dake ƙasar Andalus.
Sai dai a wannan wasa na yau ana ganin kamar wasan zai rage armashi duba da yadda aka bayyana Cesar babu babban abokin hamayyar Leonel Msssi wato Christiano Ronaldo wanda yana can a killace yana fama da cutar nan ta Coronavirus wadda itace ta hana ya buga wasan na yau.
Messi da Ronaldo dai basu taɓa fuskantar juna a wasan rukuni na gasar zakarun nahiyar turai ba, amma kuma sun haɗu had sau uku a gasar ta zakarun nahiyar turai har sau 3 guda biyu lokacin Ronaldo yana Manchester United yayin da guda ɗaya kuma lokacin yana Real Madrid.
Itama dai Barcelona babu ɗan wasan Philippe Coutinho zata buga wannan wasa sakanakon rauni daya samu. Juventus da Barcelona dai kowacce ta sami nasarar lashe wasan farko data fafata inda kowacce tana da maki guda 3 kuma kowacce tana neman nasara a wasan na yau.
Za a fafata wannan wasa a birnin Turin dake ƙasar ta Italiya da misalin ƙarfe 9:00 agogon Najeriya da Niger da Cameroon da kuma Chad. Sai dai wasa ne da akayi hasashen kowa zai iya samun nasara akan kowa.