Wata Gidauniya dake kula da kididdigar Yan wasa ta duniya ta zabi dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi a matsayin gwarzon ɗan wasa na goma sha uku a duniya, a watanni ukun farkon wannan shekara.
Ndidi ya samu maki 85.5 na Nasarar ɗebe kwallo cikin mintuna 852 da ya fafata wasa.
Babban dan wasan da ya mamaye sahun farko a cewar gidauniyar shine Lionel Messi mai maki 92.5 cikin mintuna 998 na fafata wasa.
Wannan mataki ya sa Ndidi ya zama dan wasa na uku a Gasar Firimiya inda ya ɗara Harry Kane na Tottenham da Luke Shawa na Manchester da kuma Thiago Alcantara na Liverpool.
Sauran yan wasa dake sama sun haɗa da Robert Lewandowski na Bayern Munich, sai Jorginho na Chelsea da Ruben Diaz na Manchester City da Christiano Ronaldo dake rufa musu baya.