A yau Asabar Ne ake Fafata wasan Hamayya dake ɗaukar hankalin duniyar kwallon kafa kachokam wato El-Clasico tsakanin Kungiyar Barcelona da Real Madrid
Wannan wasa dai ya daɗe yana janye hankulan yan kwallo da ma yan kallon su a kowace shekara idan ta bijiro.
Ko da yake wasan yana ɗaukar wuta a duk lokaci, to amma wani sa’in ana iya yayyafa mishi ruwa yayin da ake tsaka da fafatawa, ta hanyar toshe abokiyar karawa.
A tarihi dai Jimilla Kungiyoyin biyi sun hadu a fafatawa ɗai-ɗai har 245, inda Ƙungiyar Real Madrid take sama da takwararta ta Barcelona a samun nasara duk da cewa tazarar bai taka kara ya karye ba.
Domin ta samu nasara ne sau 97 yayin da ita juma Barcelonar ta samu nasara sau 96, gibin da Barcelonar Ka iya cike shi a karawar ta yau idan ta darje.
Baya ga wadannan nasarori dai, kungiyoyin biyu sun yi chanjaras sau 52 Jimilla a Manyan wasannin na El Clasico Kenan.
A yanzu haka Jimilla Kungiyoyin sun zura kwallaye dai-dai har 808, inda Real Madrid take da 408, yayin ƙungiyar yankin Catalan, Barcelona ke da 400 cif-cif.
Kyaftin din tawagar Real Madrid Sergio Ramos shine dai dan wasa daya tilo da ya fi kowane ɗan wasa fafata wasan na El Clasico, inda ya barje gumi sau ɗai-ɗai har sau arba’in da biyar.
Yayin da takwarar shi Gwarzon dan wasan Duniya Lionel Messi ne kuma ya fi kowanne dan wasa zura kwallo, inda yake da kwallaye 26 shi kaɗai, yawan kwallayen da babu wani dan wasa da ya kama kafar shi.