A yau Asabar za a buga wasan hamayya mai zafi a gasar Lalaiga tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona inda za a fafata wasan a filin wasa na Camp Nou dake can birnin Catalonia.
A makon daya gabata kowacce ta rasa maki 3 a wasan mako na shida, inda a yau za a iya cewa kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa zata taka leda sosai dimin taga ta sami maki 3 akan abokiyar hamatyarta.
A kakar wasan data gabata a wasanni biyu da aka fafata gida da waje Real Madrid ta sami maki 4 inda ita kuma Barcelona ta sami maki 1 daga wasanni guda biyun da suka fafata a filayen wasanni na Camp Nou da kuma Santiago.
Hamayya tsakanin Real Madrid da Barcelona ta samo asaline kan siyasa tsakanin birnin Madrid da birnin Catalonia inda har yanzu Catalonia suke iƙirarin cewar sai anbasu yankinsu ya zama ƙasarsu suma suci gashin kansu. Wannan gaba ba iya yankin ƙwallon ƙafa ta tsaya ba a’a dukkanin yankunan guda biyu gaba suke da juna ta kowacce fuska.
Za a take wannan wasa a wannan yamnaci na Asabar da misalin ƙarfe 4:00 agogon Najeriya da Niger da Cameroon da kuma Chad wato ƙarfe 3:00 dai-dai agogin GMT da Ghana.