A wannan yammaci na Lahadi za ayi karon batta mai zafi tsakanin manyan ƙungiyiyin ƙwallon ƙafa guda biyu wato Manchester United da Arsenal. Za a fafata wasan a filin wasa na Old Trafford dake birnin na Manchester na ƙasar ta Ingila.
Manchester United da Arsenal kowacce tana cikin wani hali tsakaninsu a sabuwar kakar wasan ta bana duba da yadda ake jibgar kowacce daga cikinsu. Itadai Manchester United kwata-kwata bata lashe ko wasa guda ba a gida wato filin wasanta inda tayi rashin nasara a wasanni biyu ta buga kunnen doki a wasa guda.
Haka itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal kowanne babban wasa data fafata batasami nasara ba wanda hakan babbar barazana bace a dangane da dukkanin ƙungiyar datakeson lashe gasar ta ajin Firimiya.
Za a fara fafata wasan da misalin ƙarfe 5:30 agogon Najeriya da Niger da Kamaru da kuma Chad. Wasan dai wasa ne na hamayya sosai da sosai kuma ana ganin koaacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa zata iya samun nasara.