An dage wasan kusa da na karshe na cin kofin Carabao tsakanin Liverpool, da Arsenal ranar Alhamis, Wanda shine wasan zagaye na farko.
Hukumar EFL ta amince da bukatar kungiyar Liverpool na sake tsara wasan saboda karuwar wadanda ake zargi da kamuwa da cutar COVID-19 a tsakanin ‘yan wasa da ma’aikatan bada Agaji na kungiyar.
Kungiyar Jurgen Klopp ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ta shafin yanar gizon su a yammacin yau Laraba.
Gwajin na baya bayan nan a ranar Talata ya tabbatar da adadi mai yawa, ciki har da Pepijn Lijnders, wanda zai jagoranci Liverpool a filin wasa na Emirates.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Da Ake Zargin Ƴan Ne Sun Sace ‘Yan China 2, Yayin Da Suka Harbe Masu Basu Tsaro
Barkewar cutar ta sa Liverpool ba ta da isassun ‘yan wasa da ma’aikata da za su iya cika ka’idojin gasar kamar yadda aka tsara tun farko.
Sakamakon haka, za a buga wasan farko na karawa hudu na karshe a filin wasa na Anfield ranar Alhamis 13 ga watan Janairu, da karfe 7:45 na yamma agogon GMT.
Yayin da kuma za a yi wasan na biyun ne ne a filin wasa na Emirates ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, kuma za a fara wasan da karfe 7:45 na yamma.